Rooney zai huta a wasansu da Schalke 04

rooney Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wayne Rooney

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ba zai saka Wayne Rooney ba a wasansu na ranar Laraba da Schalke 04 a gasar zakarun Turai.

Bayan da United ta samu galaba a bugun farko daci biyu da nema, Ferguson na kokarin yiwa tawagarshi garan bawul a yayinda zasu fuskanci Chelsea a karshen mako a gasar premier.

Akwai yiwuwar Dimitar Berbatov zai buga wasan da Schalke 04 da Michael Owen.

Sai dai Fabio da Silva ba zai buga ba saboda rauni.

Dan Brazil din ya jimu ne a wasansu da Arsenal, wasan daya janyowa United matsala a kokarinta na lashe gasar premier.

United a halin yanzu ta dara Chelsea da maki uku a yayinda ya rage wasanni uku a kamalla gasar premier ta bana.