Bana son in bar Leicester City-Aiyegbeni

yakubu
Image caption Yakubu Aiyegbeni

Dan kwallon Najeriya wanda ke matsayin aro a Leicester City Yakubu Aiyegbeni ya ce yana maraba da kulla yarjejeniya ta dun dun dun a Leicester din.

Dan shekaru ashirin da takwas, Yakubu ya bar Everton ne zuwa Leicester a watan Junairu.

Ya shaidawa BBC cewar"ina tunanin cewar na yi abinda ya dace dani a Everton, don haka ina son in sauya sheka".

Yakubu ya kara da cewar"idan na koma Leicester City tabbas zan ji dadi".

Yakubu ya zira kwallaye goma cikin wasanni 19 daya bugawa Leicester City cikin watanni hudu da Sven-Goran Eriksson ya dakkoshi aro.

Ya koma Everton ne daga Middlesbrough a shekara ta 2007 akan fiye da fan miliyan 11.