Makomar Blanc na cikin duhu a Faransa

blanc Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Laurent Blanc

Makomar kocin kwallon Faransa Laurent Blanc ya kara shiga cikin duhu a yayinda ake cigaba da cece-kuce a harkar kwallon kasar.

Tsohon dan kwallon Faransa wanda haifaffen Senegal ne wato Patrick Vieira ya shiga sawun masu sukar Blanc da sauran manyan jami'an kwallon kasar akan batun kayyade yawan wadanda ba 'yan asalin kasar bane da zasu din wakiltar kasar a kwallo.

Vieira na daga cikin tawagar 'yan kwallon Faransa data lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998 wacce ta kunshi 'yan asalin kasashe daban daban.

Vieira yace"nasan Lauren Blanc kuma ina jituwa da shi, bana tunanin mutum ne mai kin jinin bakake amma da mamaki irin kalamanshi".

Shima dai Lilian Thuram wanda ya takawa Faransa leda a wasanni 142 cewa yayi "Bana tunanin neman afuwa zai yanke shi saboda kalaman ya raunata shi".

Amma dai Christophe Dugarry ya maidawa Thuram martani akan cewar a lokacin da aka lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998, shi Thuram din ya gayyaci 'yan uwanshi bakake don a dauki hutu tare da kofin.