AC Milan ta lashe gasar Serie A ta Italiya

AC Milan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan AC Milan na murnar lashe gasa

AC Milan ta lashe gasar Serie A a karon farko tun shekara ta 2004 bayan ta buga canjaras tsakaninta da AS Roma a ranar Asabar.

A yayinda ya rage wasanni biyu a kamalla gasar, AC Milan nada maki 78 inda ta dara Inter da maki tara.

Wannan nasarar ta AC Milan ta kawo karshen kaka gidan da Inter Milan na lashe gasar sau biyar a jere.

Sannan kuma Massimiliano Allegri nasara ce ta farko a gare shi a kakar wasa ta farko tare da AC Milan a matsayin koci.

A halin yanzu AC Milan ta lashe gasar Serie A sau goma sha takwas kenan, amma dai Juventus itace tafi kowacce samun nasara inda ta lashe gasar sau 27.