Stoke ta kawo karshe burin Arsenal

stoke Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Inda Stoke ta jikawa Arsenal gari

Kungiyar Stoke City ta kawo karshen burin Arsenal na lashe gasar premier a bana bayan ta lallasa gunners daci uku da daya.

Kenwyne Jones da Jermaine Pennant da Jonathan Walters ne suka ciwa Stoke kwallayenta uku a yayinda Robin van Persie ya farkewa Arsenal kwallo daya.

Sakamakon ya nuna cewar Arsenal zata kara kamalla kakar wasa na shida a jere ba tare da ta lashe wani kofi ba.

*Aston Villa 1 - 1 Wigan Athletic *Bolton Wanderers 1 - 2 Sunderland *Everton 2 - 1 Manchester City *Newcastle United 2 - 1 Birmingham City *West Ham United 1 - 1 Blackburn Rovers *Tottenham Hotspur 1 - 1 Blackpool *Wolves 3 - 1 West Brom *Stoke City 3 - 1 Arsenal