Beckham ya yi hadari amma bai ji rauni ba

beckham Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption David Beckham

Tsohon kyaftin din Ingila David Beckham bai ji rauni ba bayan yayi hadari a motarshi akan titin Los Angeles a Amurka.

Motar Beckham kirar Cadillac tayi taho mu gama ne da wata motar data lalace kamar yadda kakakin 'yan sandan California ta bayyana.

Amma dai an kai direban wancen motar asibiti duk da cewar rauninshi baida tsanani.

Kakakin 'yan sandan ta ce"Ba a tsare David Beckham ba sakamakon hadarin".

Tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid Beckham mai shekaru 36 na zaune a Los Angeles tunda ya koma taka leda a Major League Soccer a Amurka tare da LA Galaxy a shekara 2007.