Manchester United na gabda lashe gasar premier

man u
Image caption Vidic ne ya ciwa United kwallo na biyu

Manchester United na bukatar maki guda ne tal a wasanta da Blackburn a ranar Asabar don lashe gasar premier a karo na goma sha tara.

United na kan hanyarta na daga kofinne bayan ta casa Chelsea daci biyu da daya a filin Old Trafford.

Javier Hernandez ne yaci kwallon farko minti daya da fara wasan bayan Park Ji-sung ya mika mashi kwallo a yayinda Nemanja Vidic yaci kwallo na biyu bayan Ryan Giggs ya bashi kwallon.

Frank Lampard ya farkewa Chelsea kwallo guda a yayinda Alex ya hana United samun kwallo na uku bayan Wayne Rooney ya kai hari.

A yayinda ya rage wasanni biyu a kamalla gasar premier, Manchester United na da maki saba'in da shida sai kuma Chelsea mai maki saba'in a yayinda Arsenal keda maki sittin da bakwai.