Muna da kwarin gwiwa kan Bale - Speed

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gareth Bale yana taka leda matuka a kakar bana

Kocin Wales Gary Speed ya ce yana fatan Gareth Bale zai warke cikin gaggawa daga raunin da ya samu a idon sahu.

Za a yi wa Bale gwaji a ranar Litinin bayan da Charlie Adam ya turbude shi a wasan Tottenham da Blackpool inda aka tashi 1-1.

Speed yana fatan dan wasan mai shekaru 21, zai buga wasannin da Wales za ta kara a gasar cin kofin FA na kasashe hudu nan gaba a wannan watan.

"Ba shi da kan jiki, domin haka ina fatan zai warke da wuri," kamar yadda ya shaida wa BBC Wales.