Manchester United ta musamman ce-Guardiola

pep
Image caption Pep Guardiola ya jinjinawa Sir Alex Ferguson

Kocin Barcelona Pep Guardiola ya yiwa Manchester United lakabi a matsayin "ta musamman" a yayinda ake cigaba da jinjinawa Sir Alex Ferguson a kokarinshi na lashewa kulob din gasar premier na 19.

Nasarar da United ta samu akan Chelsea daci biyu da daya a ranar Lahadi, ta sa United na bukatar maki daya ne tal don shiga gaban tarihin da Liverpool ta kafa a Ingila.

Guardiola wanda kungiyarshi zata fuskanci United a wasan karshe na gasar zakarun Turai a ranar 28 ga wannan watan ya ce "United nada tawaga mai karfi".

Manchester United ta samu gurbin zuwa wasan karshenne bayan ta casa Schalke 04 a zagayen kusada karshe daci shida da daya a bugu biyu inda United ta saka kananan 'yan wasanta a karawar da suka yi na biyu a Old Trafford.

A lokacin wasan an baiwa Rio Ferdinand, Nemanja Vidic, Michael Carrick, Ryan Giggs, Park Ji-sung, Wayne Rooney da Javier Hernandez hutu.