Real Madrid ta sayi Nuri Sahin daga Dortmund

sahin Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nuri Sahin

Real Madrid ta kulla yarjejeniya da dan kwallon Turkiya wanda aka haifa a Jamus Nuri Sahin daga Borussia Dortmund.

Dan shekaru ashirin da biyu, Real Madrid ta ce zai shafe shekaru shida tare da ita.

A cewar kungiyar dan wasan nada gogewa da kuma kokarin rarraba kwallo a tsakiya.

Amma dai Real din bata bayyana kudin data siyeshi ba, sai dai kafafen yada labarai na Jamus sun ce an siyeshi akan dala dubu goma sha hudu.

Sahin wanda kwangilarshi ya kamata ta kare a shekara ta 2013 a Dortmund, ya fara bugawa kulob din kwallo a shekara a 2005 tun yana shekaru goma sha shida da haihuwa.

Ya zira kwallaye shida a kakar wasa ta bana a yayinda ya taimakawa Dortmund ta lashe gasar Bundesliga a bana.

Sahin ya hade da Mesut Oezil da kuma Sami Khedira a Real Madrid wadanda suka bar taka leda a Jamus.