AC Milan ta sayi Taye Taiwo na Najeriya

tawo
Image caption Taye Taiwo

Kocin AC Milan coach Massimiliano Allegri ya bayyana cewar dan Najeriya Taye Taiwo zai hade da zakarun Italiyan bayan kamalla kakar wasa ta bana.

Dan shekaru ashirin da shida kwangilar Taiwo zata kare ne a karshen wannan watan a kungiyar Olympique Marseille ta Faransa

Allegri yace don kara karfin bayanmu mun siyo Mexes da Taiwo.

Shi kuma Mexes zai bar AS Roma ne don hadewa da Milan din.

Mexes mai shekaru 29 zai maye gurbin Alessandro Nesta ne a tsakiyar bayan AC inda za a hadashi da dan Brazil Thiago Silva.

Taiwo ya kasance dan Afrika na hudu da a yanzu ke Milan inda zai hade da dan Ghana Kevin-Prince Boateng, da dan Sierra Leone Rodney Strasser sai kuma Nnamdi Oduamadi na Najeriya.

Ya koma Marseille ne a shekara ta 2005 inda ya bugawa kungiyar kwallo a wasanni fiye da 200.