Foster zai dan dakata daga tawagar Ingila

Image caption Ben Foster

Mai tsaron gidan Birmingham Ben Foster ya ce zai dan dakata daga kamawa Ingila kwallo na wani dan lokaci.

Dan wasan ya ce yana so ya maida hankali ne a kungiyarsa ta Birmingham.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 28 ne mai tsaron gida na biyu a tawagar Ingila tun bayan an kammala gasar cin kofin duniya a bara, amma daga nan dan wasan ya yi ta fama da rauni.

Foster ya ce: "Idan kana wasa a manyan wasanni a koda yaushe, yana yawan kashe jiki.

"Ba wai kuma ina kokarin daina taka leda bane wa kasa ta gabaki daya."

Foster ya taka rawar gani a kakar wasan bana, inda kuma ya taimakawa kungiyarsa kaiwa ga wasan karshe a gasar cin kofin Carling, a yayinda kuma tayi galaba akan Arsenal.