'Ya kamata ayi sauyi a Fifa'- Bin Hammam

Image caption Bin Hammam

Dan takarar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Mohamed Bin Hammam, ya ce hukumar na bukatar sauyi domin samar da damar kawar da kaurin sunan da hukumar ta yi na zargin cin hanci da rashawa.

Dan takarar mai shekarun haihuwa 62 zai yi takara ne da shugaban hukumar mai ci yanzu wato Sepp Blatter a ranar daya ga watan Yuni.

"Ina da kwarin gwiwa kan Fifa, kuma nayi amanar cewa hukumar ce da za'a iya dogara da ita wajen daukar matakai." In ji Hammam.

"Amma ba za'a iya cewa komai na tafiya dai dai ba a hukumar, dolene kuma ayi sauyi."

A farko wannan makon ne dai mutumin da ya jagoranci kamun kafar Ingila na neman bakoncin gasar cin kofin duniya da za'a shirya a shekarar 2018 ya zargin cewa wasu jami'an Fifa sun nemi cin hanci domin baiwa Ingila damar.

Bin Hammam ya ce karkashin jagorancin Blatter, ba'a tafiyar da Fifa yadda ya kamata domin ba'a bin ka'idojin hukumar.