Nadal ya kai wasan gab da kusa dana karshe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rafeal Nadal

Rafael Nadal ya buga wasa mai kayatarwa a zagaye na uku a gasar Rome Masters inda ya doke takawarsa dan kasar Spaniard Feliciano Lopez da maki 6-4 6-2.

Nasarar da Nadal din ya samu ya bashi damar tsallakewa zuwa zagayen gab da kusa dana karshe a gasar na Rome Masters.

Dan wasan wanda shine na daya a fagen Tennis ya dan fuskanci matsala a wasan sa na farko, amma daga baya kuma sai ya mike.

Idan har Djokovic ya samu damar lashe gasar, kuma Nadal ya gaggara wace wasan dab da kusa dana karshe, Djokovic zai karbe mukamin na daya ne a fagen Tennis.