Manchester United na gabda siyen sabon gola

Edwin van der Sar

Asalin hoton, other

Bayanan hoto,

Edwin van der Sar

Shugaban Manchester United David Gill ya ce kulob din na gabda sayen gola don maye gurbin Edwin van der Sar wanda zai yi ritaya.

Dan kasar Holland din mai shekaru arba'in ya koma Old Trafford ne daga Fulham a shekara ta 2005.

Rahotanni na alakanta golan Ajax Maarten Stekelenburg, dana Atletico Madrid David de Gea da kuma na Schalke Manuel Neuer.

Tsohon golan Netherlands Van der Sar ya buga wasanni 262 a Red Devils inda ya taimaka mata ta lashe kofin premier hudu dana zakarun Turai a shekara ta 2008.

Sau biyu akan nadashi mai tsaron gida mafi bajinta a Turai.