Togo ta lashe gasar WAFU bayan doke Najeriya

siasia
Image caption Samson Siasia na baiwa 'yan Eagles umurni

Togo ta samu galaba akan mai masaukin baki Najeriya daci uku da biyu don lashe gasar kofin kasashen yammacin Afrika wato WAFU da aka buga ranar Asabar a Abeokuta.

Atakora Lalawele ya ciwa Togo kwallaye biyu sannan ya bada guda aka ci abinda ya baiwa kasar nasarar lashe gasar.

Sai kuma Bartholomew Ibenegbu ya ciwa Najeriya kwallaye biyu.

Sakamakon wasan ya kawo karshen wasanni biyar da Samson Siasia ya samu nasara tun da aka bashi jagorantar Super Eagles kuma rashin nasarar ya hanashi lashe kofinsa na farko a Najeriya.

Wannan nasarar ta baiwa Togo damar samun kyautar dala dubu ashirin da biyar sai kuma Najeriya wacce aka bata kyautar dala dubu goma sha biyar.

Liberia ce tazo ta uku bayan ta samu galaba akan Ghana daci uku da daya.