Caf:Al Alhy na rukuni guda da Esperance

caf
Image caption Kofin da kulob takwas din zasu fafata akai

Manyan abokan hammaya Al Ahly na Masar da kuma Esperance ta Tunisia na rukuni guda a gasar zakarun Afrika.

Kungiyoyin Mouloudia Alger ta Algeria da kuma Wydad Casablanca ta Morocco ko kuma Simba ta Tanzania sune cikon rukunin B.

A rukunin A kuwa akwai Enyimba ta Najeriya da Al Hilal ta Sudan da Raja Casablanca ta Morocco da kuma Coton Sport ta Kamaru.

Duk kungiyar data lashe gasar zata samu kyautar dalan Amurka daya da rabi sannan itace zata wakilci Afrika a gasar kulob kulob na duniya da za ayi a Japan.

Sai dai wacce ta lashe gasar a bara TP Mezembe ta Congo an fiddata daga gasar sakamakon hukuncin da CAF ta dauki akanta.