Watakila Fulham ta samu gurbin zuwa Europa

hughes
Image caption Kocin Fulham Mark Hughes

Akwai alamun Fulham zata samu karin gurbi daya da aka baiwa Ingila na zuwa gasar Europa bisa tsarin Uefa na yin kwallo ba tare da aikata laifuka dayawa ba.

Fulham dai itace ta biyu a gasar premier bayan Chelsea da bata laifi sosai a filin kwallo.

Tunda kuma Chelsea nada gurbin zuwa gasar zakarun Turai, shine yasa ake ganin Fulham zata iya samu.

Tottenham da Blackpool suma suna takarar duk da cewar Spurs zata iya samun gurbi idan ta karke ta biyar a gasar.

A bisa jerin da Uefa ta fitar na mutunta ka'idoji a yadda kasar ke taka leda da kuma kulob din dake cikinta, Norway ce ta farko.

Ingila ce ta zama ta biyu sai Sweden ta uku, sannan kuma an basu kyautar da'a a tawagar 'yan kwallonsu.