Ronaldo ya kafa tarihin ruwan kwallaye

Cristiano Ronaldo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cristiano Ronaldo ya taka rawa sosai a kakar bana

Cristiano Ronaldo ya shiga sahun kwararrun 'yan wasan da suka taba zira kwallaye hamsin a kakar wasa guda, bayan da ya zira kwallaye biyu a wasan Madrid da Villarreal.

Dan wasan na Portugal ya cimma wannan matsayi ne a minti na 22 lokacin da ya zira kwallon farko da bugun firikit, sannan ya kara zira wani firikit din a minti na 94.

A yanzu dan wasan ya zira kwallaye 51 a kakar bana, inda ya cimma abokin hamayyarsa Lionel Messi wanda ya cimma wannan mataki a watan Afrilun da ya gataba.

Ronaldo ya zira kwallaye 38 a gasar La Liga ta bana, inda ya kamo tarihin da Telmo Zarra da Hugo Sanchez suka kafa na zira kwallaye 38 a tarihin gasar - kuma yana da damar kafa sabon tarihi idan har ya zira kwallo a wasan karshe na gasar da ya rage.

'Yan wasa goma sha uku ne dai a tarihi suka taba zira kwallaye sama da hamsin a kakar wasa guda daya.