Watakila Tevez ya cigaba da zama a City

tevez Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Carlos Tevez

Carlos Tevez ya ce zai iya cigaba da taka leda a Manchester City idan ya samu mafita akan batun iyalanshi.

Dan kwallon Argentina din wanda ake ta alakantashi da komawa Italiya, amma bayan taimakawa City ta lashe gasar FA, Tevez ya ce ba yanzu zai tafi ba.

Tevez yace"Iyalai na sune nafi baiwa fifiko,bani da matsala da kowa a wannan kulob din saboda muna mutunta juna".

Ya kara da cewar"ban sani ba ko zan tafi Spain ko Italiya ko kuma a'a".

'Ya'yan Tevez biyu na zaune ne a Buenos Aires a Argentina.

Manchester City ta kawo karshen shafe shekaru 35 babu kofi sakamakon lashe gasar FA a ranar Asabar, sannan kuma kungiyar ta samu gurbin zuwa gasar zakarun Turai.