West Ham ta raba gari da Avram Grant

Avram Grant Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Avram Grant ya samu kansa cikin mawuyacin hali

West Ham United ta tabbatar da cewa ta raba gari da koci Avram Grant bayan da ta sha kashi a hannun Wigan da ci 3-2 abinda ya jefa ta rukunin Championship daga Premier.

Kulob din ya tabbatar da cewa kocin dan Isra'ila zai bar kungiyar sa'a guda bayan da suka sha kashi a karo na 18 a kakar bana.

"A yanzu Avram Grant ba shi ne kocin West Ham United ba," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

An nada koci Kevin Keen da ya ja ragamar kungiyar a wasan da za ta yi na karshe a Premier da Sunderland ranar Lahadi.

Tsohon kocin Chelsea da kuma Portsmouth, Grant, ya maye gurbin Gianfranco Zola ne a watan Yunin 2010 a kan kwantiragin shekaru hudu.