'Barcelona ta boye mu' :In ji Ferguson

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Alex Ferguson

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Mancester United, Sir Alex Ferguson ya bayyana Barcelona a matsayin kungiyar kwalon kafa da ta fi shahara bayan ta lalasa Mancester United da ci uku da daya a wasan karshe na gasar zakarun Turai.

Kungiyar kwalon kafan ta buga wasa me kayartarwa inda suka rika raraba kwallon ta ko'ina, abun da ya basu damar daukar kofin zakarun Turai a karo na uku a filin wasa na Wembley.

Wayne Rooney ya rama kwalon da Pedro ya saka masu a raga inda suka yi kunnen doki, sai dai kwallayen da Lionel Messi da David Villa suka jefa sune suka sa Mancester United ta kwashi kashinta a hanu.

"Babu wani wanda ya taba boye mu kamar haka,amma sun cancanci kasancewa zakarun Turai,'' In ji Ferguson.

''Sun yi wasa yadda ya kamata, kuma sun ji dadin yada suka rika buga kwallonsu. Suna daukar hankalinka da yadda suke raraba kwallo ta ko'ina kuma bamu iya takuruwa Messi ba. Sai dai mutane da dama sun fadi haka.

''A lokacin dana shafe a matsayin Koci, ita ce kungiyar kwallon kafa data fi shahara da zamu kara da ita.''

Bayan kayen da ta ba sha a hanun Barcelona a wasan karshe na zakarun Turai a birnin Rome a shekerar 2009, Ferguson ya zaku wurin ganin cewa hakan be sake fauruwa ba.