Hukumar CAF ta raba WAFU gida biyu

caf
Image caption A yanzu Wafu ta zama tarihi

Hukumar kwallon Afrika-Caf ta wargaza hukumar kwallon yankin yammacin Afrika wato Wafu.

Caf ta yanke hukuncin ne a taron data gudanar ranar Litinin a birnin Alkahira.

Sanarwar da Caf ta fitar ta ce ta dauki matakin ne don magance matsalolin da Wafu ke fuskanta, kuma za a raba yankin zuwa gida biyu.

Kafin ruguza Wafu dai shugaban hukumar kwallon Ghana Kwesi Nyantakyi ne shugabanta na riko.

A wannan makonne aka kamalla gasar kocin Wafu a Abeokuta a Najeriya inda Togo ta lashe.

A yanzu an rabba yankin zuwa gida wato Western Zone A da Western Zone B.

Yankin A ya kunshi kasashen Cape Verde, Gambia, Guinea, Guinea Bissau, Liberia, Mali, Mauritania, Senegal da kuma Sierra Leone.

Yankin B nada: Benin, Burkina Faso, Ivory Coast, Ghana, Niger, Nigeria da Togo.