FA ta gargadi Ferguson akan kalamanshi

ferguson Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sir Alex Ferguson

Hukumar dake kula da kwallon Ingila wato FA ta gargadi Sir Alex Ferguson akan yadda zai dinga yin kalamai a nan gaba, saboda irin kalaman da yayi akan Howard Webb.

Kocin Manchester United din yayi kalaman ne kafin wasan da suka doke Chelsea daci biyu da daya a ranar 8 ga watan Mayu.

Duk da cewar Ferguson yayi kalamai masu kyau akan Webb,amma ya sabawa dokar FA data ce ba'a yarda koci yayi magana akan alkalin wasa kafin fara wasa ba.

A taron da Ferguson ya kira ya bayyana cewar"zamu samu alkalin da yafi kowanne iya aiki, bani da shakku akanshi".

A kwanakin baya ne aka dakatar da Ferguson na wasanni biyar da kuma tarar fan dubu talatin saboda sukar alkalin wasa Martin Atkinson bayan da Chelsea ta doke su daci biyu da daya a watan Maris.