Japan ta fice daga gasar Copa America

Japan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Girgizar kasa ta jefa kwallon kafa a Japan cikin rudani

Shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Japan Junji Ogura ya ce kasar za ta fice daga gasar cin kofin Copa America bayan da ta aike a rubuce ga kasar Argentina.

An wallafa sakon a shafin intanet na Hukumar kwallon kafa ta Argentina a ranar Litinin, inda aka sanar da shugaba Julio Grondona cewa Japan ba za ta halarci gasar ta watan Yuli ba.

"Bayan cikakken nazari, mun fahimci cewa ba za mu iya tattara 'yan wasa domin halartar wannan babbar gasa ba, don haka wajibi ne mu fice," a cewar Ogura, yana mai bada hakuri.

Wannan mataki ya fito da yadda wasu kungiyoyin kwallon Turai ba sa so su saki 'yan wasansu na Japan su halarci wasan, da kuma yadda aka dage gasar kwallon Japan bayan girgizar kasar da aka yi a watan Maris.