Blatter zai tattauna da 'yan Afrika a Johannesburg

blatter Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sepp Blatter

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Sepp Blatter zai tattauna da shugabanni kwallon kafa na Afrika a karshen mako a birnin Johannesburg don yin kamfe su sake zabanshi.

Manufar tattaunawar itace a duba irin alfanun da aka samu sakamakon yin gasar cin kofin duniya a bara.

Har wa yau taron zai baiwa Blatter damar sake neman kuri'ar Afrika kafin zabe a ranar daya ga watan Yuni.

Dama dai hukumar kwallon Afrika wato Caf ya bayyana goyon ta akan Blatter idan ta bukaci wakilanta su zabeshi.

Sai dai Muhammed bin Hammam dan kasar Qatar nada matukar farin jini a Afrika abinda yasa ake ganin zaben zai yi zafi.