Berekum Chelsea ta lashe gasar kwallon Ghana

ghana Hakkin mallakar hoto b
Image caption Manyan 'yan kwallon Ghana

Kungiyar Berekum Chelsea ta lashe gasar kwallon premier ta Ghana.

Emmanuel Clottey wanda yafi kowanne dan kwallon zira kwallo a gasar, shine ya baiwa Berekum Chelsea nasara a wasan data doke Real Tamale United daci daya me ban haushi.

Berekum Chelsea ta lashe gasar a yayinda ya rage wasanni uku a kammalla fafatawa inda kungiyar ta shiga gaban Asante Kotoko.

Wannan ne karon farko kungiyar ta lashe gasar kwallon Ghana.

Shekaru goma sha daya da suka wuce ne aka kafa kungiyar inda wasu magoya bayan Chelsea suka kafata, kuma itace kungiyar da zata wakilci Ghana a gasar cin kofin zakarun Afrika.