Ingila ba zata yi zaben shugaban FIFA ba

Bernstein
Image caption David Bernstein shugaban FA na Ingila

Hukumar dake kula da kwallon Ingila wato FA ta yanke shawarar fasa kada kuri'a a zaben shugaban Fifa.

Sepp Blatter shugaban dake jan ragamar hukumar na fuskantar kalaubale ne daga dan Qatar Mohammed Bin Hammam, wato shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya.

Amma FA din ta ce ba zata yi zabe ba saboda zargin cin hanci da rashawa akan Fifa a watanni da suka wuce.

A ranar daya ga watan Yuni ne za ayi zaben.

Sanarwar da FA ta fitar tace"Kwamitin gudanarwar FA a ranar Alhamis ta amince da kin kada kuri'a a zaben shugabancin Fifa".

Ta kara da cewar "saboda irin batutuwan dake faruwa a kwanan nan, FA na ganin cewar da wuya ta iya goyon bayan daya daga cikin 'yan takarar".