Ba a gayyaci Osaze ba a wasan Najeriya da Argentina

osaze
Image caption Osaze Odemwingie

Najeriya da gayyaci 'yan kwallo ashirin da hudu don buga wasan sada zumunci tsakaninta da Argentina, amma babu sunan Osaze Odemwingie a cikin jerin.

Rashin kiran Odemwingie ba zai rasa nasaba da takun sakar dake tsakanin dan wasan da kocinsa Samson Siasia tun bayan kin buga wasan Najeriya da Kenya.

A cikin jerin 'yan kwallo biyu ne kacal ke taka leda a Najeriya sauran 22 din suna kwallo a Turai ne a yayinda aka saka Victor Moses da Shola Ameobi a matsayin masu jiran tsamanni don ana jiran Fifa ta amince dasu.

Moses da Ameobi sun taba bugawa ingila kwallo a sashin matasa a don haka sai hukumar kwallon Ingila ta baiwa Fifa takardar amincewarta kafin su bugawa Najeriya duk da cewar iyayensu 'yan kasar ne.

Har wa yau wadanan da aka gayyata din sune zasu bugawa Najeriya a wasanta na share fagen neman gurbin zuwa gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika a shekara ta 2012.

Cikakken jerin:

Masu tsaron gida:Enyeama Vincent, Aiyenugba Dele da kuma Ejide Austine

Masu buga baya: Chibuzo Okonkwo da Yusuf Muhammed da Taiye Taiwo da Yobo Joseph da Yusuf Ayinla da Adeleye Dele da kuma Efe Ambrose

Masu buga tsakiya: Mikel Obi da Joel Obi da Fegor Ogude da Uche Kalu da Igiebor Nosa da Oduamadi Nnamdi da Isaac Promise

'Yan gaba: Ahmed Musa da Anichebe Victor da Utaka Peter da Nsofor Obinna da Uche Ikechukwu da Ekigho Ehioson da kuma Emenike Emmanuel.