Rooney ya yi barazana ga mai binsa a dandalin Twitter

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rooney na da mabiya da dama a dandalin musayar ra'ayi da muhawara na Twitter.

Dan wasan Manchester United Wayne Rooney ya yi barazana ga wani mai binsa a dandalin Twitter inda ya rubuta masa cewa: " Zan saka barci yanzu cikin dakika goma", bayan an harzika shi a dandalin.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 25 yana da mabiya sama da 570,000, a dandalin na Twitter.

Rooney wanda yake maida martani ga mai binsa din ya ce; "Mu hadu a filin wasan horon mu, kuma da fatan ba za ka ji tsoro ba. Zan jira ka, kuma kada ga gayawa kowa."

Daga baya dai Rooney ya bada hakuri a dandalin inda ya kyalkecewa da dariya sannan ya ce shima ya rama ne.

Rooney ya share sunan mai binsa din a shafinsa na Twitter.