Chelsea ta kori Carlo Ancelotti

ancellottui Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Carlo Ancelotti

Chelsea ta kori kocin 'yan kwallonta Carlo Ancelotti bayan buga kakar wasa ta bana babu nasara daga kowanne kofi.

Sanarwar da Chelsea ta fitar ta yiwa Ancelotti fatan alheri musamman tarihin lashe kofin biyu da yayi a bara.

Dan shekaru hamsin da daya kamata yayi kwangilarshi ta kare a Chelsea a shekara mai zuwa.

A baya an yita yada jita-jita akan cewar idan Ancelotti ya kamalla kakar wasa ta bana babu kofi za a sallameshi.

Tsohon kocin Chelsea Avram Grant shima haka aka yi mashi a shekara ta 2008 inda ya karke na biyu sannan aka dokesu a gasar zakarun Turai.

Tsohon kocin AC Milan din a watan Yulin shekara ta 2009 ne ya koma Stamford Bridge a kwangila ta shekaru uku.