Blackpool da Birmingham sun koma Championship

premier
Image caption West tun a makon daya gabata ta koma Championship

Blackpool da Birmingham City zasu koma buga gasar Championship bayan sun nitse daga gasar premier ta Ingila.

Ita dai Blackpool ta sha kashi ne a wajen Manchester United daci hudu da biyu a yayinda Birmingham ta sha kashi a hannun Tottenham daci biyu da daya.

Wolverhampton Wanderers kuwa zata cigaba da buga gasar premier duk kashin data sha a wajen Blackburn Rovers daci uku da biyu.

Itama Wigan bazata bar premier ba sakamakon nasararta akan Stoke City daci daya me banhaushi.

Sakamakon wasu daga cikin karawar premier: *Aston Villa 1 - 0 Liverpool *Bolton Wanderers 0 - 2 Manchester City *Everton 1 - 0 Chelsea *Fulham 2 - 2 Arsenal *Manchester United 4 - 2 Blackpool *Newcastle United 3 - 3 West Brom *Stoke City 0 - 1 Wigan Athletic *Tottenham Hotspur 2 - 1 Birmingham City *West Ham United 0 - 3 Sunderland *Wolves 2 - 3 Blackburn Rovers