Lille ta lashe gasar Faransa a karon farko tun 1954.

lille Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lille ne zakarun Faransa

Lille ta lashe gasar kwallon Faransa a karon farko tun shekarar 1954.

Kungiyar ta lashe gasar ne bayan ta tashi biyu da biyu tsakaninta da Paris Saint-Germain.

A yayinda ya rage karawa guda a kamalla gasar, Lille ta shiga gaban Marseille da maki shida, bayan da ita Marseille ta buga biyu da biyu tsakaninta da Valenciennes.

Ludovic Obraniak da Moussa Sow sune suka zira kwallayen daya baiwa Lille kafina biyu a karon farko cikin shekaru 65.

Obraniak a makon daya gabata shine yaci kwallon daya baiwa Lille nasara akan PSG don lashe gasar kofin Faransa.

Kocin Lille Rudi Garcia yace"kakar wasa ta bana tayi mana dadi matuka".