Blatter ba zai samu duka kuri'un Afrika ba-Papoe

blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Blatter da Hammam

Babu tabbas akan cewar Sepp Blatter zai samu duka kuri'un Afrika a zaben Fifa a mako mai zuwa, in ji wani jami'an kwallon Ghana.

Fred Papoe mataimakin shugaban hukumar kwallon Ghana-GFA ya amince akan cewar akwai yiwuwar wasu kasashen su zabi Hammam a Afrika.

Papoe na daga cikin wakilan Afrika 37 da suka ce zasu zabi Blatter a yayinda zai fafata da dan Qatar Mohammed Bin Hamman.

Papoe ya kara da cewar"kowa ya amince da hukuncin da aka yanke amma akwai shakku tunda anki sanya hannu".

Masu sharhi na ganin cewar Blatter da gaggarumin rinjaye zai lashe zaben Fifa a karo na hudu a yayinda za ayi zabe a ranar daya ga watan Yuni a Zurich.