An baiwa Ferguson da Vidic kyautar bajinta

Sir Alex Ferguson da Nemanja Vidic Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sir Alex Ferguson da Nemanja Vidic

An baiwa kocin Manchester United Sir Alex Ferguson kyautar manaja mafi bajinta a gasar premier a yayinda Nemanja Vidic ya samu kyautar a banagaren 'yan kwallo.

Wannan ne karo na goma da Ferguson ya samu kyautar a bukin da wakilan kungiyoyi da 'yan jarida da masu kallon kwallo ke kada kuri'a, shi kuma Vidic wannan ne karo na biyu daya samu.

A bana ne mutanen biyu suka taimakawa United ta lashe gasar premier a karo na 19 a Ingila.

Kungiyar na saran kara samun nasara a kakar wasa ta bana inda zata fuskanci Barcelona a wasa karshe na gasar zakarun Turai a filin Wembley a ranar Asabar mai zuwa.

Sai dai ita kungiyar kwarrarrun 'yan kwallo Gareth Bale na Tottenham ne samu kyautar a yayinda ita kuma kungiyar maruba kwallo suka zabi Scott Parker na West Ham.