Nicklas Bendtner na son barin Arsenal

bendtner
Image caption Nicklas Bendtner

Mahaifin Nicklas Bendtner wanda kuma shine wakilin dan kwallon, ya bayyana cewar danshi ya bayyanawa Arsenal aniyarsa ta barin kulob din.

Dan kwallon Denmark din, bai tsinci kanshi ba a Arsenal a kakar wasa ta bana saboda galibi akan benci ake barinshi.

Bendtner ya nuna damuwa akan kin bashi damar taka leda sosai kuma yana jiran tayi daga wajen kulob daban daban a yayinda rahotanni suka nuna cewar Bayern Munich na zawarcinshi.

Thomas Bendtner yace"Nicklas nada niyyar sauya kulob dari bisa dari, ya yanke shawara kuma ya gayama Arsenal".

Mahaifin nashi ya kara da cewar"Nicklas na bukatar taka leda akan kari".

A cewarshi akwai sha'awa akan dan kwallon daga wajen kungiyoyi daga Ingila da Jamus.