U21:An cire sunayen Wilshere da Carroll

wilshere
Image caption Jack Wilshere

An cire Jack Wilshere da Andy Carroll cikin tawagar 'yan kwallon Ingila da zata buga gasar cin kofin Turai na 'yan kasada shekaru 21 da za ayi a Denmark.

A baya dai kocin Arsenal Arsene Wenger yayi kakausar suka akan saka Wilshere mai shekaru 19 cikin tawagar.

Kocin matasan Ingila Stuart Pearce yace"ya bayyana mani cewar a watan Maris cewar yanason kasancewa cikin tawagar amma a yanzu baida sha'awar buga gasar".

Shima dan wasan Liverpool Carroll an cire sunanshi ne saboda rauni kuma rashinsu ba karamin cikas bane ga Pearce.

Kocin a baya ya saka sunayen Wilshere da Carroll cikin 'yan kwallo 40 kafin ya tantance 23 da zasu wakilci Ingila a Denmark.