Bin Hammam ya bukaci Ingila ta canza shawara

hammam
Image caption Mohammed Bin Hammam

Dan takarar shugabancin Fifa Mohamed Bin Hammam ya bukaci hukumar kwallon Ingila FA ta sake shawararta akan batun fasa kada kuri'a a zaben Fifa.

Hukumar FA ta yanke shawarar kin shiga zaben ranar daya ga watan Yuni saboda zargin cin hanci akan Fifa.

Amma Bin Hammam wanda zai fafata da Sepp Blatter yace yaji mamakin hukuncin.

Yace"abin takaici ne FA ta yanke shawarar kin gwada kawo canji ta cikin gida".

Matakin FA din bai rasa nasaba da fushin kasa samun damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018, inda Rasha ta samu damar.

Bugu da kari jami'an Qatar sun musanta zargin cewar sun bada kudi ne aka zabesu na samun damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya da za ayi a 2022.

Jami'an na Qatar sun soki jaridar Sunday Times saboda kasa bada cikakken bayanai akan zargin bada cin hanci akan Issa Hayatou and Jacques Anouma.