Wasanmu na United sai an tashi-Mascherano

Javier Mascherano Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Javier Mascherano da Pep Guardiola

Javier Mascherano yace babu zabi tsakanin Barcelona da Manchester United a yayinda zasu fuskanci juna a wasan karshe na gasar zakarun Turai a ranar Asabar a Wembley.

Yace"a wasan karshe babu kungiyar da zake ce tayi zarra saboda kowacce nasara tana neman nasara ne".

Manchester United da Barcelona duk sun lashe gasar cikin gidansu kuma duk su biyun na neman lashe gasar a karo na hudu.

United na kokarin ramuwar gayya bayan kashin data sha a wajen Barcelona a wasan karshe na shekara ta 2009.

Mascherano, wanda ya fafata da United sau dayawa a lokacin da yake Liverpool yace yanasaran wasa mai zafi tsakanins da yaran Sir Alex Ferguson.

Tarihin nasarorin kungiyoyin biyu a gasar zakarun Turai:

* Barcelona - 1992, 2006 and 2009 * Man Utd - 1968, 1999 and 2008