Fifa na binciken Warner da Hammam

Warner da Hammam Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jack Warner da Muhammed Bin Hammam

Fifa ta soma gudanar da bincike akan zargin cin hanci akan manyan jami'anta hudu hadda mataimakin shugaba Jack Warner da dan takarar shugabancin hukumar Mohamed bin Hammam.

Wani jami'in kwamitin gudanarwar Fifa Chuck Blazer shine ya gabatar da zargin akansu.

Blazer yayi zargin cewar an sabawa dokar Fifa a taron da Bin Hammam da Warner suka shirya. Sauran wadanda ake zargin sune Debbie Minguell da Jason Sylvester daga hukumar kwallon yankin Caribbean.

Anyi taronne a ranakun 10 da 11 ga watan Mayu akan batun zaben shugabancin Fifa da za ayi a ranar 1 ga watan Yuni.

A ranar 29 ga watan Mayu ne jami'an hudu zasu kare kansu a gaban kwamitin da'a na Fifa.

Fifa ta sanarda cewar Petrus Damaseb dan kasar Namibia shine zai ji ba'asin wadanda ake zargin saboda shugaban kwamitin Claudio Sulser dan kasar Switzerland.