Man United na gab da sayen David de Gea

David de Gea Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai kalubale a gaban David de Gea na maye gurbin Edwin Van der Sar

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson, ya tabbatar da cewa yana gab da sayen golan Atletico Madrid David de Gea.

United ta dade tana neman gola domin ya maye gurbin Edwin Van der Sar, wanda zai yi ritaya a karshen kakar bana.

"Mun dade muna tattaunawa kan batun," a cewar Ferguson bayan wasan girmama Gary Neville a ranar Talata.

"Matashi ne, kuma ya kware, don haka zai iya maye gurbin Van der Sar."

De Gea ya taka leda sau 45 a Atletico Madrid a bana, inda ya taimakawa kulob din ya kare a mataki na bakwai a gasar La Liga.

Sai dai har yanzu bai kai ga takawa babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar Spain leda ba.