Blatter zai gurfana a gaban kwamitin bincike

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Fifa, Seff Blatter

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta FIFA, ta fara gudanar da bincike kan shugabanta Seff Blatter, a wani bangare na fadada binciken da ake yi kan zargin cinhanci.

FIFA ta gayyaci Mr Blatter ya gurfana a gaban kwamitinta na da'a ranar Lahadi, bayanda wani mamba a kwamitin gudanarwa ya yi korafi a kansa.

A farkon makonnan ne FIFA ta kaddamar da bincike kan mutumin da ek kalubalantar Seff Blatter a zaben shugabancin kungiyar Mohamed Bin Hammam.

Mr Blatter ya ce ba zai ce uffan ba kafin zaman jin ba'asin na ranar Lahadi.