Binciken harin NATO a Afghanistan

Image caption Mutanen Afganistan suna zanga-zangar nuna bakin cikin harin NATO

Dakarun kasashen duniya a Afghanistan da kuma gwamnatin kasar sun ce suna gudanar da bincike akan rahotannin da suka ce wani hari ta jirgin sama ya kashe farar hula goma sha hudu a kudanci kasar.

Kakakin dakarun karkashi jagrorancin kungiyar NATO ,Tim James ya ce an tura wata tawaga zuwa wurin da abun ya faru a Nawzad dake yankin Helmand.

Sai dai kakakin kananan hukumomi Dawood Ahmadi ya ce mutane akala goma sha hudu, inda dukaninsu mata da yara ne aka kashe a harin da aka kaiwa gidajen farar hula su biyu a ranar asabar.