Scholes ya yi ritaya daga kwallon kafa

Paul Scholes
Image caption Scholes ya fara taka wa United leda ne a 1994, inda ya buga wasanni 676

Dan wasan Manchester United Paul Scholes ya bada sanarwar yin ritaya daga kwallon kafa yana mai shekaru 36 da haihuwa.

Scholes ya fara taka wa United leda ne a 1994, inda ya buga wasanni 676, kuma ba zai shiga sahun kociyoyin kungiyarba.

Matakin ya zo ne bayanda dan wasan ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar League a Ingila a karo na 19, 10 daga ciki a lokacinsa, kuma wasansa na karshe shi ne na gasar zakarun Turai da suka sha kashi a hannun Barcelona a ranar Asabar.

"Wannan ba mataki bane dana dauka gaba-gadi, ina ganin a yanzu ne ya fi dacewa na daina taka leda," a cewar Scholes.

Ya kara da cewa: "Kasancewa cikin wadanda suka taimaka aka lashe gasar League sau 19, ba karamar nasara ba ce."

Kocin United Sir Alex Ferguson ya jinjinawa dan wasan, inda yace "ba karamin kwararren dan wasa ba ne.