Ba zan yi ramuwar gayya ba - Blatter

Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sepp Blatter ne kawai ya tsaya takara a zaben da aka yi

Shugaban Hukumar FIFA Sepp Blatter, ya ce ba zai yi ramuwar gayya a kan Ingila ba, duk da kokarin da ta yi na hanawa a zabe shi a karo na hudu.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ta yi kokarin dakatar da zaben amma sai ragowar kasashe suka yi watsi da bukatar a babban taron da aka yi a birnin Zurich.

Blatter ya nuna matukar mamaki kan matakin na FA amma ya ce ba zai kullaci Ingilan ba.

"Ba zan nuna damuwa kan Hukumar kwallon da bata zabe ni ba," a cewarsa.

"Ni shugaba ne na kowa-da-kowa, kuma zan yi aiki tare da kowa, ina farin ciki cewa kasashe 186 sun zabe ni. Kada ka damu da Ingila.

"Hukumar FA ita ce ta daya a duniya - wacce aka kafa a 1863, su suka kirkiro da kwallo - sun cancanci a kira su FA. Kamata ya yi su zama abin koyi.

"Na samu labari, kuma Uefa ta yi kokarin sasantawa. Na zaci za a sansanta, don haka na yi mamaki lokacin da suka yi yunkurin dakatar da zaben."

Karin bayani