FIFA na gab da sake zaben Blatter

Shugaban FIFA Seff Blatter Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Seff Blatter da kuma FIFA na fuskantar babban kalubale

Babban taron Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ya amince a gudanar da zaben shugabancin kungiyar a ranar Laraba, duk da korafin da hukumar FA ta Ingila ta gabatar.

Shugaban hukumar ta FIFA, Sepp Blatter na kan hanyarsa ta sake darewa shugabancin hukumar a karo na hudu, saboda shi kadai ne ya ke takara a zaben.

Babban mai adawa da shi Muhammad Bin Hammam ya janye daga takarar, kafin daga bisani a dakatar da shi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Sa'o'i kafin a fara zaben Blatter ya shaida wa babban taron cewa, shi ne kawai zai iya kawo sauye-sauyen da ake bukata a hukumar ta FIFA.

Sannan ya yi alkawarin dawo da kimar Hukumar, yana mai cewa zai sauya yadda ake zabar kasar da za ta dauki nauyin gasar cin kofin duniya.

Ko a ranar Talata sai da hukumar kwallon kafa ta Ingila, da takwararta ta yankin Scotland suka bukaci a dakatar da zaben, saboda zarge-zargen cinhanci a Fifar.

Wakilan kasashe 172 ne daga cikin 208, suka yi watsi daga bukatar ta Ingila, yayin da 17 suka goyi baya, inda wasu 17 suka kaurace daga zaben, sai kuma wakilai biyu da basu da damar kada kuri'a.

Zargin cinhancin ya sanya Fifa ta dakatar da manyan jami'anta guda biyu, wato Muhammad Bin Hammam da Jack Warner daga cikinta.

Karin bayani