Balotelli ya kara turgude gwiwarshi ta dama

maro Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mario Balotelli

Dan kwallon Manchester City Mario Balotelli ya kara jin sabon rauni a gwiwarshi ta dama lokacin horo a sansanin Italiya.

Dan shekaru ashirin din ya jimu ne lokacin wasansu da 'yan kwallon Ingila 'yan kasada shekaru 18.

A don haka ba zai buga wasan Italiya da Estonia ba a ranar Juma'a na neman gurbin zuwa gasar cin kofin kasashen Turai, kamar yadda ba zai buga wasansu da Jamhuriyar Ireland ba.

Likitan 'yan kwallon Italiya Enrico Castellaci yace"Na damu matuka amma zan tattauna da likitocin City".

Balotelli ya koma City daga Inter Milan akan fan miliyan 24 a shekara ta 2010 kuma sau biyu ana mashi tiyata a gwiwarsa ta hagu.

Ya zira kwallaye goma tun zuwansa City.