Carrick ba zai bugawa Ingila wasa ba

Image caption Michael Carrick

Dan wasan Manchester United, Michael Carrick ba zai samu taka leda ba a wasan share fage na gasar cin kofin Turai ta shekarar 2012 da Ingila za ta buga da Switzerland a ranar asabar.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 29, yana fama da rauni ne sanadiyar raunin da ya samu a wasan karshe da United ta buga da Barcelona da Wembley a gasar zakarun Turai.

Carrick dai ya halarci sansanin horon 'yan gudun hijira, amma saboda raunin da yake da shi.

David Stockdale da Jermain Defoe ma bazasu samu buga wasan ba.