Owen zai kara shekara guda a Manchester United

owen
Image caption Micheal Owen

Michael Owen ya sabunta yarjejeniyarshi na karin shekara guda a Manchester United.

Dan kwallon mai shekaru talatin da daya kwangilarshi ta kare a karshen kakar data wuce amma sai ya bayyana cewar yanason ya cigaba da taka leda a Old Trafford.

Owen ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar "Na ji dadi zan cigaba da zama na karin shekara guda".

Owen dai ya shafe kusan daukacin kakar wasa ta bana ne akan benci saboda Wayne Rooney da Javier Hernandez da kuma Dimitar Berbatov.

A kakar wasa ta 2010/2011, Owen ya buga wasa sau 17 inda yaci kwallaye biyar.

Har wa yau Owen ya takawa Ingila a wasanni 89 ya koma United ne bayan ta buga kwallo a Real Madrid da Newcastle da kuma Liverpool.