Kocin Fulham Mark Hughes ya yi murabus

hughes
Image caption Mark Hughes

Kocin Fulham Mark Hughes ya yi murabus kasada shekara guda daya koma kulob din.

Ana alakanta Hughes ta zama kocin Aston Villa, amma Villa din ta karyata batun zawarcin dan kasar Wales din.

Dan shekaru 47 din ya karyata zargin cewar sai da wani kulob ya tuntubeshi kafin yayi murabus.

Yace"A matsayi na na matashin koci mai son cigaba, ina da sha'awar samun karin gogewa".

Fulham dai ta soma tattaunawa da Hughes don ya sabunta yarjejeniyarshi na karin wasu shekaru biyu masu zuwa

Tsohon kocin Manchester City din dai ya karawa Fulham karfi bayan da Roy Hodgson ya koma Liverpool.